2 Corinthians 13

1Wannan ne karo na uku da nake zuwa gare ku, ‘’Ana tabbatar da kowanne zargi ta bakin shaidu biyu ko uku.‘’ 2Na riga na yi magana a baya da wadanda suka yi zunubi da kuma sauran a lokacin da ina tare da ku karo na biyu, kuma ina sake fadi: Idan na sake zuwa, ba zan raga masu ba.

3Ina fadi maku wannan ne domin kuna neman shaida ko Almasihu na magana ta bakina. Shi ba kasashshe bane zuwa gare ku. Maimakon haka, Shi mai iko ne a cikin ku. 4Domin an gicciye shi cikin kasawa, amma yana da rai ta ikon Allah. Don mu ma kasassu ne a cikin shi, amma za mu rayu tare da shi cikin ikon Allah dake cikinku.

5Ku auna kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya. Ku yi wa kanku gwaji. Ba ku lura da cewa Yesu Almasihu yana cikin ku ba? Yana cikin ku, sai dai in ba a amince da ku ba. 6Gama ina da gabagadin cewa za ku iske an amince da mu.

7Ina addu’a ga Allah cewa ba za a same ku da laifi ba. Ba wai ina rokon mu bayyana kamar mun ci gwadawar ba. Maimakon haka, ina addu’a ku yi abinda ke dai dai, ko dayake mun yi kamar mun fadi gwadawar. 8Domin bamu iya yin wani abu na tsayayya da gaskiya ba, sai dai mu yi domin gaskiya.

9Muna farin ciki idan mun kasa ku kuma kun yi karfi. Muna addu’a kuma domin ku kammalu. 10Na rubuta wadannan abubuwa yayinda ba ni tare da ku, saboda yayin da zan kasance da ku ba zan zamar maku mai fada ba. Ba na so inyi amfani da ikon da Ubangiji ya bani in tsattsaga ku, sai dai in gina ku.

11A karshe, ‘yan’uwa, ku yi farinciki, ku yi aiki don sabuntuwa, ku karfafa, ku yarda da juna, ku zauna cikin salama. Kuma Allahn kauna da salama zai kasance tare da ku. 12Ku gai da juna da tsattsarkar sumba.

13Masu bi duka suna gaishe ku. 14Bari alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.

Copyright information for HauULB